Dangote da Bill Gates za su tallafa wa yaki da Maleriya

A Najeriya an sake sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin wasu gwamnatocin arewacin kasar da kuma gidauniyar
Dangote da ta attajirin nan mai kamfanin Microsoft, Bill Gates.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne domin yaki da zazzabin cizon Sauro da kuma ci gaba da yaki da cutar shan Inna.

Gwamnonin jihohin Borno da Yobe da Kano da Sokoto da kuma Kaduna ne suka sanya hannu a yarjejeniyar.

Wasu sarakunan gargajiya na yankin ma sun halarci taron wanda aka yi shi a ranar Laraba, a Kaduna.

Cutar shan Inna da zazzabin cizon sauro na daga cikin cututtukan da suka addabi Najeriya musamman ma arewacin kasar, kuma sun hallaka mutane da dama.

Sai dai a baya-bayan nan hukumomi sun ce an samu nasarar kawar da cutar shan Inna.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s